Me ya sa ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere ke neman a saki Nnamdi Kanu?

Ana ci gaba da tafka muhawara kan kiran da ƙungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere ta yi tana buƙatar a shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta sakin jagoran IPOB, Nnamdi Kanu.

Tsagin ƙungiyar da ke ƙarƙashin jagorancin Pa Ayo Adebanjo ne ya bayyana haka a wata sanarwa da suka fitar.

An dai san ƙungiyar ne wajen fafatukar kare muradun Yarabawa, wanda hakan ya sa wasu suka fara tunanin ko akwai wani auren siyasa da ake yunƙurin haɗawa ne da wannan tsakanin Yarabawa da ƙabilar Igbo.

Ƙungiyar ta bayyana cigaba da riƙe Kanu a matsayin rashin adalci, sannan ta bayyana shi a matsayin wanda ake riƙewa saboda siyasa.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne bayan wani taro da ta yi a gidan shugabanta, Adebanjo a jihar Ogun a ranar 28 ga Janairu.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa babu tabbacin za a yi wa Kanu adalci a kotu saboda yadda dambarwar da dama suka dabaibaye shari'ar.

"Saboda buƙatar adalci da kuma neman sulhunta ƙasar nan, Afenifere na kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta sakin Nnamdi Kanu. Babu wani dalilin ci gaba da riƙe shi ba tare da ya fuskanci shari'a ba," kamar yadda takardar da suka fitar ta nuna.

Me ya sa Afenifere ta nemi wannan buƙatar?

Domin jin me wannan kira na ƙungiyar Yarabawa ke nufi a siyasance, BBC ta tuntuɓi Farfesa Tukur Abdulkadir, malami a sashen kimiyyar siyasa a jami'ar jihar Kaduna, inda ya ce ba abin mamaki ba ne domin sun yi wannan kira a baya suna buƙatar a saki Nnamdi Kanu.

Sai dai ya ce ƙungiyar ta rabu kashi biyu ne, "tsagin Adebanjo ne suke wannan kira, kuma dama ana ganin kamar suna adawa da gwamnati domin ko a zaɓen 2023 ana ganin ba su goyi bayan Tinubu ba, Peter Obi suka gaya wa baya," in ji shi.

Ya ce a siyasance yanzu ba su da rinjaye idan aka kwatanta su da ɗaya ɓangaren, kuma tasirinsu ragagge, "ba mu dai san nan gaba ba."

A game da ko ana ƙoƙarin ƙulla wani auren siyasa ne tsakanin manyan yankunan guda biyu, ya ce babu wannan, domin a cewarsa, "babu yadda za a yi wanda ba ya tare da gwamnati ya iya haɗa alaƙa ingantacciya, kuma ga shi su ba wasu cikakkun ƴan adawa ba ne."

Ya ce a dai matakin gwamnati ana hasashen akwai wannan yunƙurin na ƙulla alaƙa da yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.

Ya ce, "amma dai Afenifere ɓangaren Adabanjo ba su da wani tasiri da kaifin siyasa da za a ce idan suna goyon bayan abu, zai yi tasiri. Wannan bai da bambanci da tatsuniya. Sai kana da jama'a ne za ka iya ƙulla alaƙa da wani ɓangare domin cimma wasu muradu," in ji Farfesa Abdulƙadir.

Rikicin shugabanci a Afenifere

Afenifare

Asalin hoton,Afenifare

Sai dai ita ƙungiyar ta kare muradun Yarabawa tana fama da rikicin shugabanci wanda yake yi wa harkokin ƙungiyar tarnaƙi.

A wasiƙar da ƙungiyar ta fitar na buƙatar a saki Kanu, ta kuma sanar da naɗa lauya, Dele Farotimi a matsayin sakataren tsare-tsarenta.

Sai dai ɗaya ɓangaren, wanda ke ƙarƙashin shugabancin Pa Reuben Fasoranti, ya fito ya bayyana cewa shugabancin wancan tsagin ba halastacce ba ne, don haka naɗa sabon sabon sakataren tsare-tsaren bai da amfani.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da tsagin Fasoranti ya fitar bayan wani taro a Ijebu-Igbo da ke Ogun, wanda sakataren tsare-tsaren tsagin na Fasoranti, Abagun Kọle Ọmọlolu ya fitar.

Ko a watan Maris na shekarar 2023, lokacin da Tinubu ya lashe zaɓen shugaban ƙasa, Pa Ayo Adebanjo, ya bayyana zaɓen da ya bai wa Tinubu nasara a matsayin mai cike da kura-kurai.

Ya ce sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba abu ne da za a amince da shi ba, kuma hakan na iya haifar rikici a ƙasar.

Sai dai kafin zaɓen, ƙungiyar ta Afenifere, wadda ake tunanin tana da alaƙa ne da tsagin Fasoranti ta nuna goyon bayanta ga Bola Tinubu.

Comments

Popular posts from this blog

Kano Gov Launches Biometric Software (KIPPIS) for Civil Servants, Pensioners, Others

2025 JAMB START SELLING FORM ONLINE E-PIN