Me ya sa ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere ke neman a saki Nnamdi Kanu?
Ana ci gaba da tafka muhawara kan kiran da ƙungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere ta yi tana buƙatar a shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta sakin jagoran IPOB, Nnamdi Kanu. Tsagin ƙungiyar da ke ƙarƙashin jagorancin Pa Ayo Adebanjo ne ya bayyana haka a wata sanarwa da suka fitar. An dai san ƙungiyar ne wajen fafatukar kare muradun Yarabawa, wanda hakan ya sa wasu suka fara tunanin ko akwai wani auren siyasa da ake yunƙurin haɗawa ne da wannan tsakanin Yarabawa da ƙabilar Igbo. Ƙungiyar ta bayyana cigaba da riƙe Kanu a matsayin rashin adalci, sannan ta bayyana shi a matsayin wanda ake riƙewa saboda siyasa. Talla Ƙungiyar ta bayyana haka ne bayan wani taro da ta yi a gidan shugabanta, Adebanjo a jihar Ogun a ranar 28 ga Janairu. Ƙungiyar ta ƙara da cewa babu tabbacin za a yi wa Kanu adalci a kotu saboda yadda dambarwar da dama suka dabaibaye shari'ar. "Saboda buƙatar adalci da kuma neman sulhunta ƙasar nan, Afenifere na kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta sakin Nnamdi K...